Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - An tsara Mista Abdollahian, zai gana da manyan jami’an kasar ta Azerbaijan inda zasu tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi alakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma batutuwan da suka shafi yankin.
Dama kafin hakan ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya gana da takwaransa na Azerbaijan a daura da taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, a Islamabad, inda suka tabo batutuwa da dama da suka shafi kasashen dama alakar dake tsakanin Bakou da Tehran.
342/